Dec 16, 2018 12:21 UTC
  • Amurka Ta Kai Hari Akan Masallacin Garin Hajin Da Ke Kasar Syria

Jiragen yakin kawancen da Amurka take jagoranta a kasar Syria ne su ka kai wa masallacin garin Hajin hari, da ke gundumar Deir Zur

Amurka ta riya cewa harin ya zo ne a karkashin abin da ta kira yaki da ta'addanci

A ranar 7 ga watan Disamba ma, kawancen na Amurka ya kai wani harin akan masallacin garin na Hajin

A wasu lokutun Amurkan kan yi amfani da bama-bamai da aka kera daga sanadrin  Phosphorus wajen kai hare-hare a cikin kasar Syria

Gwamnatin Syria ta sha gabatar da koke a gaban Majalisar Dinkin Duniya dangane da hare-haren na Amurka da kawayenta wanda ba ya bisa dokokin kasa da kasa

Tags

Ra'ayi