Dec 16, 2018 14:23 UTC
  • Yemen : Ana Cikin Zaman Dar-dar A Hodaida, Bayan Barkewar Fada

A Yemen, ana cikin zaman dar-dar bayan samun rahotannin barkewar fada tsakanin bangarorin dake rikici a kasar duk da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Bayanai daga kasar sun ce an yi ta jiyo karan harbe-harbe mayan bindigo da kuma hare-haren sama a birnin Hodeida, lamarin dake zaman kalubale ga yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin suka cimma a shiga tsakanin MDD, a ranar Alhamis data gabata.

Ko wanne daga cikin bangarorin biyu na zargin juna da keta yarjejeniyar da aka cimma.

Kamfanin dilancin labaren Saba mallakin 'yan Houtsis ya bayyana cewa jiragen kawacen da Saudiyya ke jagoranta ya ci gaba da kai hare-haren sama a yau Lahadi a birnin na Hodeida, tare da zargin dakarun dake biyaya ga gawmnatin kasar da kai hare hare a wasu anguwanni dake birnin.

A ranar Alhamis data gabata ne bangarorin dake rikici da juna a kasar ta Yemen suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin na Hodeina da ya kunshi tashar jiragen ruwa wanda kuma ta nan ne ake shigar da galibin kayan abinci dana agaji.

Da yake bayyani kan sake barkewar rikicin, babban sakatare na MDD, Antonio Guterres, ya nuna fargaba akan yiyuwar sake tabarbarewar al'amuran jin kai a wannan kasar ta Yemen, a cikin shekara 2019 mai shirin kamawa idan yunkurin cimma yarjejeniyar zaman lafiyar da ake nema ya cutura.

Ra'ayi