Dec 17, 2018 06:37 UTC
  • Shugaban Kasar Sudan Umar Albashir Ya Kai Ziyara Kasar Syria

A jiya ne shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya kai wata ziyarar aiki a kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a yayin ziyarar da shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya kai a jiya a birnin Damascus na kasar Syria, ya gana da takwaransa na kasar ta Syria shugaba Bashar Assad.

A yayin ganawar tasu, shugabannin kasashen na Syria da Sudan, sun tabo muhimman batutuwa da suka shafi halin da kasashen larabawa suke ciki, da kuma wajabcin kawo karshen abubuwan da suke a matsayin manyan matsalolin da kasashen na larabawa suke fuskanta.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da wani shugaban wata kasa ta larabawa ya kai kasar Syria, tun bayan barkewar rikici a kasar a cikin watan Maris na 2011, wanda wasu daga cikin kasashen larabawa suka da kuma Amurka gami da wasu kasashen turai da suka hada da Faransa da Birtaniya, suka yi amfani da 'yan ta'adda da nufin kifar da gwamnatin kasar ta Syria.

Ziyarar ta lbashir wata babbar alama ce da ke nuni da irin nasarar da gwamnatin kasar Syria ta samu wajen rusa dukkanin shirin da aka yi a kan kasar da nufin rusa ta, sakamakon irin matsayar da take dauka wajen kin mika kai buri ya hau dangane da manufofin Amurka da Isra'ila  a yanin gabas ta tsakiya.

Ra'ayi