Dec 31, 2019 19:07 UTC
  • Mazauna Garin Kamishli Na Syria Sun Yi Zanga-zangar Yin Tir Da Barazanar Turkiya

Masu Zanga-zangar sun yi tir da barazanar da Turkiya take yi na cewa za ta kai hari a gabacin tafkin Euphrates, suna masu jaddada cewa duk wani yunkuri na mamayar wani yanki na Syria ba zai yi nasara ba

Masu Zanga-zangar sun bayyana cewa sojojin Syria ne kadai wadanda za su iya tabbatar da tsaro da samar da hadin kai a cikin kasar.

Turkiya ta sanar da shirinta na kai farmaki akan kungoyin Kurdawa na PKK da kuma Kurdish Labour Party.

A cikin shekaru biyu a jere, sojojin Turkiya sun kutsa cikin iyakokin kasar Syria da tsawon kilo mita 2000 tare da shimfida ikonsu a cikin garuruwan al-Bab, Jarablus da Afrin.

Gwamnatin Syria wacce ta mayar da hankali wajen fada da kungiyoyin 'yan ta'adda tana daukar kutsen na sojojin Turkiya a cikin kasarta a matsayin mamaya 

Tags

Ra'ayi