Jan 02, 2019 17:17 UTC
  • Saudiyya: A Yau Ne Aka Cika Shekaru 3 Da Kisan Sheikh Nimr Baqir Nimr

A yau ranar 2 ga watan Janairu 2019 aka cika shekaru 3 da kisan gillar da masarautar Al Saud ta yi wa Sheikh Nimr Baqir Nimr.

Al'ummar yankin Awamiyya da ke gabashin kasar saudiyya a yau suna juyayin tunawa da cikar shekaru uku na kisan gillar da masarautar kasar ta yi wa babban malamin addinin musulunci Sheikh Nimr Baqir Nimr a ranar 2 ga watan Janairun 2016.

Sheikh Nimr dai yana daga cikin malamai da suke gaya wa sarakunan Saudiyya gaskiya dangane da zalunci da rashin adalcin da suke yi, musamman a kan marassa rinjaye a kasar, da hakan ya hada da mabiya mazhabar shi'a, wadanda su ne kashi 15 cikin dari na al'ummar kasar, inda yake yin kira da a yi adalci a tsakanin dukkanin 'yan kasa baki daya, ba tare da tauye wa wani hakkinsa na dan kasa ba.

Wannan ya sanya sarakunan masarautar Al saud sun ta kame shi tare da tsare shi a lokuta daban-daban, amma bayan hawan sarki Salman mai ci a yanzu, ya bayar da umarni da a sare masa kai da takobi.

Dukkanin arzikin danyen man fetur da iskar gas da tattalin arzikin kasar saudiyya ya dogara a kansu, ana fitar da su ne daga yankunan mabiya mazhabar shi'a da ke gabashin kasar ta Saudiyya.

Tags

Ra'ayi