Jan 09, 2019 07:14 UTC
  • Sojojin Rasha Sun Fara Sintiri Akan Iyakar Kasar Syria Da Turkiya

Sojojin Rasha sun fara sintirin ne dai a daidai lokacin da kasar Turkiya take barazanar shiga cikin yankin Manbaj domin yakar rundunar kurdawa

Kungiyar Kurdawan Syria ta YPG ta kira yi sojojin gwmanatin Syria da su ba ta kariya daga barazanar da kasar Turkiya take yi musu

Kakakin sojan kasar Rasha Yosov Mamtov ya bayyana cewa sojojin Rasha sun shiga yankin Manbaj da ke kan iyaka da kasar Turkiya

Mamtov ya kara da cewa; manufar shiga yankin shi ne tabbatar da tsaro da kuma sanya idanu akan abinda ke kai da komawa

A ranar 28 ga watan Disamba ne dai sojojin gwamnatin Syria su ka shiga cikin garin na Manbaj tare da daga tutar Syria a cikinsa

Tags

Ra'ayi