Jan 11, 2019 12:09 UTC
  • Kasar Lebanon Za Ta Kai Karar Isra'ila A Gaban Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar koli ta tsaron kasar Lebanon ta ce za ta kai harar ne saboda keta hurumin kasar da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi

A jiya alhamis ne sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da suke akan iyaka sun kafa shinge-shinge 12 a cikin yankin da ake da sabanin iyaka akansu, a kusa da garin Udaisah da ke kudancin Lebanon

A wani bayani da Majalisar koli ta tsaron kasar ta Lebanon ta fitar a jiya alhamis bayan zaman gaggawa da ta yi a karkashin shugaban kasa Micheal Aun, ta sanar da cewa; Abin da 'yan sahayoniyar su ka yi, keta hurumin kasar Lebanon ne sannan kuma take kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701 ne

Majalisar tsaron kasar ta Lebanon ta bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kuma dakarun zaman lafiya da suke a Lebanon da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu na tabbatar da zaman lafiya da aiki da kuduri mai lamba 1701

 

Tags

Ra'ayi