Jan 19, 2019 06:56 UTC
  • Mayakan Hashdushabi A Iraqi Sun Kashe Yan Ta'adda 35 A Cikin Kasar Siriya

Komandan dakarun mayakan sa kai na Hashdushabi a yankin Ambar na kasar Iraqi ya bada sanarwan kashe mayakan kungiyan yan ta'adda ta daesh su 35 a cikin kasar Siriya a Jiya Jumma'a da dare.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Qasim Muslih yana cewa bayana sun sami bayanai masu inganci dangane da yunkurin mayakan ta na kawo masu farmaki daga Suse na kasar Siriya, sun yiwa sansaninsu luguden wuta da makaman atilari, wanda ya kai ga mutuwar akalla mayaka 35 daga cikinsu da kuma raunata wasu 41.

Qasim Muslih ya kara da cewa daga cikin wadanda suka halaka a harin na jiya, har da Abu Waddah, da kuma Abu -Hamza wadanda suka kasance komandojin a kungiyar yan ta'adda da Abu-Futum.

Komandan Hashdushabi a yankin Ambar ya kammala da cewa mayakansa suna kula da kai-kawon yan ta'adda a yankunan kan iyakar kasar da kasar Siriya, sannan ya zuwa yanzu sun halaka yan ta'adda da dama a kasar ta Siriya. 

Kafin haka dai dakarun na Hashdudhabi sun sami izini, sannan suna aiki tare da jami'an tsarin kasar Siriya a duk hare-haren da suke kaiwa yan ta'addan a cikin kasar ta Siriya. 

 

Tags

Ra'ayi