Feb 18, 2019 04:14 UTC
  • Yaki Bai Kare Ba A Siriya, Inji Assad

Shugaba Bashar Al-Assad, na Siriya ya bayyana cewa har yanzu da sauren aiki game da yakin da kasarsa ke fama dashi.

Mista, Assad wanda ke bayyana hakan jiya Lahadi, a wani jawabi gaban wakilan kananen hukukomi na kasar, ya ce kasarsa na fama da nau'ukan yake yake guda hudu, da suka hada dana soji, da tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaba Assad, ya kuma ja hankalin Kurdawa wandanda bai fayyace su ba da cewa Amurka dake shirin janyewa daga kasar ba ta basu kariya, tare da shawartarsu akan kada su dogara da Amurka, don kuwa gwamnatin Siriya ce kawai zata iya kawo masu tsaro da kuma zaman lafiya.

A hannu guda kumaa, shugaba Assad, ya yi kakkausan suka kan shugaba, Recep Tayyip Erdogan, na Turkiyya, wanda ya zarga da cewa wani karamin jami'in Amurka ne, wanda ya ce yana rarashin mahukuntan Washington akan  su bashi dabar shiga arewacin kasar ta Siriya.

Kalamman na Assad dai na zuwa ne a daidai lokacin da Turkiyya, ta bayyana anniyarta, ta kafa wata iyaka ta tsaro mai fadin kilomita talatin a cikin kasar ta Siriya, wanda kuma a cewarsa ga Kurdawan idan baku kare kasarku ba, to kuwa zaku kasance bayun Turkiyya.

Tags

Ra'ayi