Feb 18, 2019 19:27 UTC
  • Poland Ta Kirayi Jakadan Isra'ila Domin Nuna Takaici

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Poland ta kirayi jakadan Isra'ila a kasar domin nuna masa takaicin kasar kan irin kamalan da suka fito daga bakin ministan harkokin wajen Isra'ila na rikon kwarya Katsap.

A cikin kalamasa na baya-bayan ministan gwamnatin yahudawan ya bayyana kasar Poland da cewa, al'ummar kasar da su da 'yan Nazi duk su guda ne, suna tsananin kiyayay da yahudawa.

Wannan furuci ya bakantawa hukumomin kasar ta Poland, wanada hakan ya sanya firayi ministan kasar ya sanar da cewa ya fasa halartar zaman taron da aka shirya gudanarwa a Isra'ila, tare da halartar kasashen Hungry, Solvakia, Chek da kuma Poland, wanda kuma hakan yasa sauran kasashen ma suka dage halartar tasu.

A cikin wanann makon ne Poland ta dauki nauyin wani taro da Amurka ta shirya domin nuna kiyayya ga kasar Iran, wanda aka shirya da sunan duba batun tsaro a yankin gabas ta tsakiya, inda taro kaco kaf ya yi dirar mikiya  akan kasar Iran, tare da kauda ido daga dukkanin ayyukan cin zalun da Isra'ila take yi a kan al'umar palastine, da kuma kasashen yankin da suka kirkiro kungiyoyin 'yan ta'adda masu akidar kashe bil adama da sunan jihadi.

 

 

 

 

 

Ra'ayi