Aug 18, 2016 05:35 UTC
  • Kasar Rasha Ta Musanta Ikirarin Amurka Na Cewa Ta Karya Dokar Majalisar Dinkin Duniya

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta mayar da martani ga ikirarin kasar Amurka na cewa ta karya kudurin kwamitin tsaron MDD ta hanyar amfani da da filin jirgin saman kasar Iran wajen kai hari kan 'yan ta'addan kungiyar Da'esh (ISIS) a kasar Siriya tana mai kiran Amurkan da ta sake duba kudurin kwamitin tsaron.

Kamfanin dillancin labaran Tas na  kasar Rashan ya jiyo kakakin ma'aikatar tsaron kasar Rashan Igor Konashenkov yana cewa koda wasa kasar Rasha ba ta karya kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231 ba da Amurkawan suke ishara da shi, don haka ya bukace su da su sake dubi cikin kudurin da kyau.

Har ila yau ministan harkokin wajen Rashan ma Sergei Lavrov yayi watsi da wannan zargi na Amurkan inda ya ce koda wasa gwamnatin Rasha ba ta taka kudurin kwamitin tsaron MDD ba ta hanyar amfani da filin jirgin saman Iran wajen kai hare-hare ta sama da 'yan  ta'addan ISIS din a Siriya.

A jiya ne dai kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurkan Mark Toner ya ce akwai yiyuwar kasar Rasha  ta karya kudurin MDD wanda daga cikin abin da ya kumsa har da batun haramta cinikayyar makamai da Iran ko kuma taimaka mata wajen karfafa karfinta na soji, lamarin da jami'an Rashan suka yi watsi da shi.

A shekaran jiya ne dai jami'an Iran suka sanar da cewa gwamnatin kasar  ta amincewa sojojin kasar Rasha su yi amfani da filin jirgin saman kasar wajen kai hare-hare ta sama a kan 'yan ta'addan kasar Siriya a ci gaba da aiki tare da ke gudana tsakanin kasashen biyu da nufin kawo karshen 'yan ta'adda a yankin.

Tags

Ra'ayi