• Kotun ICC Tace Akwai Yiyuwar Ta Hukunta 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'esh

Babbar mai shigar da kara a kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffukan yaki ICC, Fatou Bensouda ta bayyana cewar kotun tana shirye-shiryen hukunta 'yan ta'addan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da aka kama.

Kamfanin dilancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar babbar mai shigar da karar a kotun na ICC Fatou Bensouda tana ci gaba da shirye-shiryen neman hanyoyin da za a bi wajen hukunta 'yan ta'addan kungiyar Da'esh da suka fito daga kasashe daban-daban na duniya suke aikata ta'addanci a kasashen Siriya da Iraki.

Madam Fatou Bensouda ta ci gaba da cewa kotun ta ICC tana da hurumin bin diddigi da hukunta 'yan kasashen waje da suke gudanar da ayyukan ta'addanci karkashin kungiyar ta Da'esh.

Duk da cewa kasashen Siriya da Iraki ba su sanya hannnu kan yarjejeniyar Roma da ta kafa kotun ta ICC ba, to amma masana shari'a sun bayyana cewar kotun tana da hurumin hukunta 'yan ta'addan da suka shigo wadannan kasashe biyu daga wasu kasashe na daban na duniya da kuma aikata ayyukan ta'addanci.

Nov 23, 2016 05:29 UTC
Ra'ayi