• Shugaban Ivory Coast Ya Aiko Da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Ayatullah Rafsanjani

Shugaban kasar Ivory Coast Alassan Ouattara ya bayyana aihininsa dangane da rasuwar shugaban majalisar fayyace maslahar Musulunci ta kasar Iran Ayatullah Ali Akbar Hashemi Rafsanjani.

Kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya bayyana cewar shugaban kasar Ivory Coast Alassan Outtara ya bayyana hakan ne cikin wata wasikar ta'aziyya da ya aike wa takwararsa na Iran Dakta Hasan Ruhani inda yayin da yake bayyana alhini da bakin cikinsa yayin da ya sami labarin rasuwar Ayatullah Rafsanjanin ya bayyana cewar: A daidai wannan lokaci na tsananin bakin ciki, ina mika sakon ta'aziyya ta a gare ka da kuma sauran al'ummar Iran saboda wannan babban rashi da aka yi.

Har ila yau a cikin wasikar tasa, Shugaba Outtara yayi fatan gafara da rahamar Ubangiji ga marigayi.

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai Ayatullah Hashemi Rafsanjanin ya rasu yana dan shekaru 82 a duniya sakamakon matsalar bugu zuciya da ya fuskanta. A yau din nan ne dai aka bisne shi a hubbaren marigayi Imam Khumaini (r.a) bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi masa salla.

Kafin rasuwarsa dai Ayatullah Rafsanjani ya rike mukamai da dama da suka hada da shugaban kasar, shugaban majalisar dokoki, shugaban majalisar kwararru ta jagoranci, mataikamin babban kwamandan soji na Iran, da kuma shugaban majalisar fayyace maslahar Musulunci ta kasar Iran.

Jan 10, 2017 17:05 UTC
Ra'ayi