• Mutanen Kasar Cypros Sun Gudanar Da Zanaga Zangar Neman Hadin Kan Kasar

Yan Kabilar Turkawa da kuma na kibilar Girkawa a kasar Cypros sun gudanar da zanga zanga a birnin Nicuziyoi na kasar don nuna goyon bayansu ga hadewar bangarorin kasar don tabbatar da dunkulewarta.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewa kabilun biyu sun bayyana goyon bayansu ga Nicos Anastasiades dan kabilar girkawa  da kuma Mustafa Akinci dan kabilar turkawa wadanda suke kokarin hada kan mutanen kasar da kuma yankunan arewa da kudancin kasar.

Kafin haka dai shuwagabannin kabilun biyu sun fara tattaunawa kan wannan batun a birnin Geneva na kasar Austria don ganin kasar Cypros ta dawo dunkulelliyar kasa.

A shekara ta 1974 ne dai gwamnatin kasar Turkia ta mamaye arewacin kasar Cypros bayan wani jyin mulkin da aka yi a kasar don hana kasar ta Cypros dunkulewa da kasar girka su zama kasa guda.  

Jan 11, 2017 06:19 UTC
Ra'ayi