• Shugaban Kasar Venezuela Ya Tuhumi Majalisar Dokokin Kasar Da Kokarin Yi Masa Juyin Mulki

Shugaban kasar Venezuela Nicola Madoro ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar wacce wakilan jam'iyyun adawa suka fi rinjaye a cikinta ta so ta yi masa juyin mulki.

Kamfanin dillacin labaran Spotnik Ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Talaka, ya kuma kara da cewa majalisar dokokin kasar karkashun shugabancin wakilan jam'iyyun adawa sun yi kokarin kwace mulki daga hannusu ta hanyar kada kuri'ar kawar da shi a majalisar a ranar litinin da ta gabata.

Shugaba Nocola Madoro ya bayyana cewa matakin da majalisar ta dauka na kauda shi baya bisa ka'ida kuma dole ne a hukunta wadanda suke karya dokokin kasa. 
Kafin haka dai wata babban koton kasar ta yanke hukuncin cewa majalisar dokokin kasar bata da hurumin tube shugaban kasa ta hanyar kada kuri'a wanda ta yi a ranar litinin.

 

Jan 11, 2017 06:20 UTC
Ra'ayi