• Shugaba Vladimir Putine na Rasha (hagu) da takwaransa na Iran Hassan Ruhani (dama)
    Shugaba Vladimir Putine na Rasha (hagu) da takwaransa na Iran Hassan Ruhani (dama)

A ci gaba da ziyarar aikin da yake a birnin Moscow, shugaban kasar Iran Hassan Ruhani ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putine inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen biyu.

Gidan talabijin din kasar Rasha ya rawaito shugaba Putine na fadar cewa ''Iran babbar abokiyar huldarmu ce, wace muke da daddiyar hulda da ita a bangarori da dama'' 

Kasashen Iran da Rasha dai na da mahanga guda akan barazana ta'addanci, kana kuma dukkansu suna adawa da duk wani yunkuri na canza fasaliwa iyakokin yankin.

Kafin hakan dai shugaba Ruhani ya gana da firaministan kasar ta Rasha Dmitri Medvedev inda ya yi fatan shinfida wani sabon babi a alakar dake tsakanin kasashen biyu ciki harda lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin kasar Syria cikin gaggawa.

Wannan ziyara wacce ita ce irinta ta farko ta Mista Ruhani a matsayinsa na shugaban kasar Iran nada manufar kara inganta huldar dake tsakanin bangarorin biyu ta fuskar tattalin arziki da kuma sauren fagage.

Mar 28, 2017 16:21 UTC
Ra'ayi