Apr 03, 2017 11:00 UTC
  • Rasha : Zargin Iran Da Ayyukan Ta'addanci, Shirme Ne, Inji Lavrov

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergueï Lavrov, ya yi watsi da zargin da Amurka kewa Iran kan aikata ayyukan ta'addanci da cewa batu ne marar tushe.

A cewar Mista Lavrov Iran kasa ce mai karfin fada aji a yakin da ake yi  da 'yan ta'adda.  

A wata hira da  mujjalar ''The National Interest'' ta Amurka, Lavrov ya ce Iran tana da karfin fada aji a yakin da ake yi da 'yan ta'adda a Syria.

Abun tuni a cewarsa babu wata hujja a cikin furcin na AMurka da kawayanta akan zargin Iran da taimakawa ayyukan ta'addanci, inda ya kara da cewa hadin gwiwa kasarsa da Iran na kara haifar da da-mai-ido a yaki da ta'addanci a Syria kuma Iran ta shiga yakin ne bisa gayyatar  gwamnatin Syria.

Tags

Ra'ayi