Apr 13, 2017 11:13 UTC
  • Ci Gaba Da Zanga-Zangar Nuna Kiyayya Ga Gwamnatin Venezuala

Majiyar tsaron Venezuala ta sanar da cewa: Zanga-zangar nuna kiyayya ga gwamnatin kasar ta fara kamari a yankunan da suke kewaye da birnin Caracas fadar mulkin kasar.

Majiyar tsaron Venezuala ta sanar da cewa: Dauki ba dadi tsakanin 'yan adawa da suke rayuwa a yankunan da suke kewaye da birnin Caracas fadar mulkin kasar Venezuala da jami'an 'yan sandan kasar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla hudu tare da jikkatan wasu adadi na daban a jiya Laraba.

Mafi yawan al'ummun da suke rayuwa a yankunan da suke kewayen da birnin Caracas fadar mulkin kasar Venezuala, al'ummu ne da suka fi fama da talauci a kasar, kuma mafi yawansu magoya bayan shugaban kasar ne Nicolas Maduro.

Rikicin baya-bayan nan ya kunno kai ne a Venezuala sakamakon matakin da kotun kolin kasar ta dauka na rage karfin Majalisar Dokokin kasar amma bayan boren 'yan adawa alatilas kotun ta sanar da yin watsi da matakin da ta dauka a baya.   

Tags

Ra'ayi