Apr 23, 2017 05:22 UTC
  • Yan Adawa A Venezuala Sun Fara Gangami Domin Kai Wa Ga Manufofinsu A Kasar

Yan adawar Venezuala sun fara gudanar da wani gagarumin gangami na sai baba ta gani a sassa daban daban na kasar domin ganin sun tursasa wa gwamnatin kasar ta amsa bukatarsu ta gudanar da zabe kafin wa'adinsa.

Rahotonni daga Venezuala suna bayyana cewa: Tun a jiya Asabar gungun 'yan adawar Venezuala sanye da fararen tufa sun fara gudanara da taron gangami a sassa daban daban na kasar musamman a harabar majami'u na mabiya addinin kirista da nufin ganin sun tursasa wa gwamnatin Nicolas Maduro hanzarta gudanar da zabuka a kasar kafin wa'adinsu.

Gwamnatin 'yan gurguzu ta Venezuala dai tuni ta yi tofin Allah tsine boren 'yan adawar kasar tare da zargin majami'un kasar da hannu a kara tunzura al'umma kan irin munanan matakan da suke dauka da suka yi hannun riga da tsarin dimokaradiyya a kasar.

A tsawon makonni uku da 'yan adawar Venezuala suka kwashe suna gudanar da zanga-zanga a sassa daban daban na kasar akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da daba suka samu raunuka.

Tags

Ra'ayi