Apr 23, 2017 11:45 UTC
  • Gwamnatin Kasar Venezuela Ta Zargi Wasu Kafafen Yada Labarai Da Tallafawa Yan Adawar Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Venezuela Delcy Rodriguez ya zargi wasu kafafen yada labarai a kasar da kuma na kasashen waje wajen tallafawa yan adawar kasar da kuma rashin fadar hakikanin abinda ke faruwa a kasar a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya ministan yana fadar haka ne a jiya Asabar ya kuma kara da cewa wasu kafafen yada labarai na ci da wajen kasar suna ta aibata gwamnatin Nikola Madurus dangene da rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnatinsa da bangaren yan Adawa tun farkon wannan watan.

Tun farkon wannan Afrilu da muke ciki ne dai magoya bayan yan adawa a kasar Venezuela suke zanga zanga a duk fadin kasar inda suke bukatar shugaban Nikolas Madoro ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar. 

Jami'an gwamnatin kasar Venezuela daga ciki har da shi shugaban kasa suna ganin gwamnatin kasar Amurka ce take goyon bayan yan adawa wadanda suke son kifar da gwamnatin kasar.

Tags

Ra'ayi