Jun 13, 2017 17:56 UTC
  • Kungiyar OPEC Ta Ce Amurka Ce Take Dagula Kasuwar Danyen Man Fetur A Duniya

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC ta bayyana cewa kasar Amurka ce ta dagula lissafinta na kyautatuwan farashin danjen man fetur a kasuwannin duniya sanadiyyar yawan man da take haka a cikin gida.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto kungiyar tana fadar haka a rahoton wata wata da take fitarwa kan yadda harkokin kasuwanncin mai fetur yake tafiya a kasuwannin duniya. 

Rahoton ya kara da cewa duk kokarin da kasashen kungiyar suka yi ta yi a cikin yan watannin da suka gabata don ganin farashin danyen man fetur ya kyautatu a kasuwannin duniya, ya kasa samar da ci gaban da take tsammani don fidda danyen man fetura mai yawa wanda kasar Amurka ta yi a cikin watanni hudu na farko a wannan shekarar.

A ranar 25 ga watan mayun da ya gabata ne wakilan kungiyar ta OPEC 25 suka amince da rage ganga milion 1.2 daga danyen man da suke haka a ko wace rana don kyautata farashinsa a duniya.  

Tags

Ra'ayi