• An Fara Zanga Zangar Ranar Qudus Ta Duniya A Birnin London

An gudanar da zanga zangar ranar Qudus ta duniya a birnin London na kasar Britania a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayyana cewa musulmi masu azumi, wadanda suka hada da limaman masallatai, yan kungiyoyin kare hakkin bil'adama da yahudawan da basa da ra'yim sahyoniya da kuma wakilan kungiyoyi daban daban sun halarci wannan zanga zangar.

An fara zanga zangar ne a kusa da ginin BBC a tsakiyar birnin London don nuna rashin amincewa kan yadda BBC take shiru kan irin ta'asan da HKI take aikatawa a Palasdinu. Banda haka masu zanga zangar sun kawo karshenta ne a ofishin jakadancin Amurka a birnin London inda masu jawabai da dama suka yi Allah wadai da Allah don irin goyon bayan da ba iyaka da take bawa HKI.

Jun 19, 2017 06:50 UTC
Ra'ayi