• Rasha Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Cuba Kan Takunkuman Da Amurka Ta Dora Mata

Gwamnatin kasar Rasha ta bayyana goyon bayanta ga kasar Cuba dangane da sabbin takunkuman da gwamnatin shugaba Donal Trump ta dora mata. Ta kuma bayyana hakan a matsayin bude wani yanayi na cacan baki tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha tana fadar haka a wani bayanin da ta fitar a jiya Lahadi. Bayanin ya kara da cewa gwamnatin Rasha tana daukar kasar Cuba a matsayin kasa mai son sulhu da zaman lafiya kuma abokiyar tafiya.

Ma'aikatar ta jaddada cewa gwamnatin kasar Rasha bata goyon bayan duk wani nau'ii na takunkumi ko kellacewa da gwamnatin Amurka tayi wa kasar Cuba.

A ranar jumma'a da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kafa dokar takaita tafiye tafiye tsakanin kasar da kasar Cuba wanda tsohon shugaban kasar Amurka Barak Obama ya bude.

 

Jun 19, 2017 06:52 UTC
Ra'ayi