• Mutane Da Dama Suka Ji Rauni Bayan da  Wata Motar Bus Ta Hau Kansu A London

Mutane da dama ne suka ji rauni a lokacin da wata motar Bus ta hau kan mutane wadanda suke barin wani masallaci a arewain London a safiyar yau Litinin.

Majalisar musulmi ta kasar Britania ta bada sanarwan cewa motar ta buge mutane wadanda suka kammala sallah a masallacin Finsbury Park daga arewacin London wanda ya kasance cikin manya manyan masallatai a birnin.

Jaridan Sun ta kasar Britania ta bayyana cewa akwai yiyiwan mutane biyu sun mutu a wannan harin. Jami'an tsaro dai killace wurin suna kuma gudanar da bincike ya zuwa yanzu ance sun kama mutum guda. Wani wanda ya ganewa idanunsa ya ce ya ga sanda motar mai farin penti ta buge mutane sannan ta wuce amma bai ga direban ba. Wani kuma ya ce bayan bugewar wani mutum ya fita daga mutar ya kuma cakawa mutum guda ko fiye da haka wuka. Kasar Britania dai musamman birnin Londan tana fama da hare haren yan ta'adda a cikin yan watannin da suka gabata.

Har yanzun babu wani labari kan wadandasuka kaiwa masallatan hari.

 

Jun 19, 2017 06:52 UTC
Ra'ayi