Jun 25, 2017 08:52 UTC
  • A Yau Ne Ake Gudanar Da Bukukuwan Salla Karama A Mafi Yawan Kasashen Musulmi

Ana gudanar da bukukuwan idin karamar salla a yau a mafi yawan Kasashen musulmi da aka sanar da ganin wata a jiya.

Tashar Al-alam ta bayar da rahoton cewa, kasashen musulmi da dama da suka hada da na larabawan yankin gabas ta tsakiya da kuma wasu na arewacin Afirka, sun sanar da ganin watan Shawwala  jiya Asabar.

A tarayyar Najeriya da Jamhuriyyar Nijar da mafi yawan kasashen Afirka a yau ne ake gudanar da idin karamar salla.

Yayin da wasu kasashen da suka hada da Iran, Oman, Libya, Morocco suka sanar da cewa ba a samu ganin wata a cikin kasashensu ba, a kan haka yau Lahadi za su cika azumi na Talatin, inda za su yi salla a gobe Litinin.

Tags

Ra'ayi