Aug 01, 2017 07:28 UTC
  • Jamus Ta Yi Kakkausar Suka Kan Sabbin Takunkuman Amurka A Kan Rasha

Gwamnatin kasar Jamus ta yi kakkausar suka dangane da sabbin takunkuman da Amurka ta dora wa kasar Rasha, tare da bayyana hakan da cewa ya sabawa ka'ida.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya bayar da rahoton cewa,a  ministan harkokin wajen kasar Jamus Sigmar Gabriel ya bayyana cewa, Amurka tana hankoron ganin ta kawo cikas ne ga kasuwar iskar gas tsakanin Rasha da kuma kasashen kungiyar tarayyar turai, wanda hakan ya saba wa duk wata ka'ida da doka ta duniya.

Ya ce yana fatan Trump zai sake yin nazari a kan wannan batu, domin kuwa hakan ba maslaha ce ga kowa ba.

A nasa bangaren shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya umarci jami'an diflomasiyyar Amurka 755 da suke kasar Rasha da cewa su bar kasar.

Tags

Ra'ayi