Aug 02, 2017 07:52 UTC
  • Bukatar Jamus Ga Tarayyar Turai Na Ta Dauki Mataki A Kan Amurka

Ministan harkokin tattalin arziki na kasar Jamus ta bayyana cewa takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar Rasha basa bisa ka'ida sun kuma sabawa dokokin kasa da kasa, ta kuma bukaci tarayyar Turai ta dauki mataki na maida martani kan Amurkan.

Brigitte Zypries, ta kara da cewa, banda kasancewar wadan nan takunkuman sun sabawa dokokin kasa da kasa, takunkuman da aka dorawa Rasha sharar fage ne na dorawa kamfanonin kasar Jamus takunkumi. Ta  ce  dokokin Amurka sun bada daman Amurka ta dorawa hatta kasar Jamus takunkumi, don haka ne ma Amurka take gargadi da kuma tambihi wa kamfanonin kasarJamus kan sabawa takunkuman da ta dorawa kasar Rasha. 

Gwamnatin kasar Jamus tare da shuwagabannin kamfanonin kasar Jamus dai sun bayyana cewa takunkuman da majalisar sanetocin Amurka ta amince da su a cikin kwanakin da suka gabata, suna iya hana su shiga cikin aikin shimfida bututun gas daga kasar Rasha zuwa tarayyar Turai wanda ake kira Nord Stream 2, wanda kuma ya zama wajibi don kare bukatun kasashen na Turai, musamman Jamus na iskar gas. 

Korafin jami'an gwamnatin kasar Jamus , musamman ita ministan tattalin arziki ya nuna cewa wadannan takunkuman da Amurka ta dorawa Rasha sun hada har da kamfanonin kasashen Turai, wanda ya nuna cewa dokokin cikin gida na kasar Amurka sun zama na kasa da kasa, don sun shafi bukatun sauran kasashen duniya wadanda suka hada har da na tarayyar Turai.

Ganin cewa sabani na dada karuwa tsakanin Amurka da tarayyar Turai, kama daga ficewar Amurka daga yerjejeniyar dumamar yanayi ta Paris, zuwa walwalan kasuwanci, ga kuma na takunkuman da Amurka ta dorawa tarayyar Rasha a yanzu, wadannan matsalolin sun taru sun zama abubuwan da suke dada nisantar da Amurka daga kawayenta na Turai. 

Ganin cewa kasar Rasha tana daga cikin kasashen duniya da suka fi yawan man fetur da iskar gas a duniya, kuma ita ce take samar da kashi 30% na iskar gas ga kasashen Turai, dorawa kamfanin makamashita takunkumai, babu makawa zai shafi tarayyar Turai. Banda haka Amurka tana gasa da Rasha a wannan fagen. 

Masana tattalin arziki a tarayyar Turai suna ganin wadannan takunkumai na Amurka kan Rasha, suna nufin fadada tattalin arzikin kasar Amurka a Turai ne, don kamfanoninta zasu maye gurbin na Rasha da turawan ne, da kuma fitar da kamfanonin makamashi na kasashen Turai wadanda suka dade suna aiki tare da tokororinsu na kasar Rasha daga aiki.. 

Wani masanin tattalin arziki dan kasar Faransa mai suna Francis Prine ya ce dole ne kasashen turai su manta da sabanin da ke tsakaninsu, su kuma fito fili su fadawa Amurka kan cewa takunkuman da ta dorawa Rasha suna barazana ga tattalin arzikin kasashensu nan gaba. 

Har'ila yau muna iya daukar cewa takunkuman da Amurka ta dorawa Rasha kamar takurawa kasashen Turai ne, don haka idan Amurka ta dage kan aiwatar da wadan nan takunkuman, to kuwa, yakamata kasashen Turai su dauki matakin maida martani ga Amurkan.

Tags

Ra'ayi