• An Gano Kuma An Bata Wani Shirin Harin Ta'addanci A Kasar Rasha

Jami'an tsaron kasar Rasha sun bada sanarwan gano da kuma bata wani shirin kai harin ta'addanci a cikin daya daga cikin tashoshin jiragen kasa na Metro a birnin Sient Perters burg a yau asabar.

Kamfanin dillancin labaran Lantaru, ya bada labarin cewa an kama yan ta'adda 7 a safiyar yau Asabar, a lokacinda suke kokarin dasa nakiya kan hanyar jirgin kasa na Metro a birnin Seint-Petresburg, inda suka lalata shirin.

Majiyar ta kara da cewa yan ta'addan yayan kungiyar Daesh na Asia Karama, sun kafa wani karfe a kan layin dogo da nufin kifar da jirgin kasan da zai wuce ta kan layin, sannan sun cika wata mutar bus da boma bomai wadanda zasu shigo da ita cikin birnin don aiwatar da wani aikin da'addancin, amma shima jami'an tsaron sun hana hakan aukuwa. 

A watannin baya dai daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hare haren ta'addancin a tashoshin jiragen kasa na Metro a birnin Sient Peters Burg na kasar Rasha   

Aug 12, 2017 17:44 UTC
Ra'ayi