• Yan Ta'adda Daga Kasashen Turai Kimani 2500 Suka Yi Yaki Tare Da'esh A Kasashen Siriya Da Iraqi

Jami'i mai kula da yaki da ayyukan ta'addanci a kungiyar tarayyar Turai ya bayyana cewa yan ta'adda daga kasashen turai kimani 2500 ne suka je kasashen Siriya da Iraki don yaki a bangaren kungiyoyin yan ta'adda a kasashen

Kamfanin dillancin Labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto  Gilles de Kerchove yana fadar haka a yau Talata ya kuma kara da cewa kungiyar Daesh tana amfani da duk wanda ta samu a cikin yan makonni don aiwatar da aikin ta'addanci. Sannan suna amfani da kafar sadarwa ta Internet don samu da kuma horar da yan ta'adda.

Gilles de Kerchove ya ce akwai yiyuwan kungiyar Daesh ta kai karin hare hare a kasashen Turai nan gaba.. Da dama daga cikin gwamnatocin kasar Turai sun tallafawa kungiyoyin yan ta'adda wadanda suke yaki da gwamnatocin kasashen Siria da Iraqi a cikin shekaru 5 da suka gabata, amma bayan da gwamnatocin wadan nan kasashe suka fi karfinsu a halin yanzu suna komawa kasashensu inda suke zama matsala a garesu. 

Sep 12, 2017 18:57 UTC
Ra'ayi