• Antonio Guterres Ya Jaddada Goyon Bayansa Kan Warware Rikicin Venezuala Ta Hanyar Lumana

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada goyon bayansa ga shirin gudanar da zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin Venezuala da 'yan adawar kasar da nufin neman hanyar warware rikicin siyasar kasar ta hanyar lumana.

A bayanin da ya fitar a daidai lokacin da ake shirye-shiryen fara gudanar da zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin Venezuala da 'yan adawar kasar a Jamhuriyar Dominica a yau Laraba: Antonio Guterres ya jaddada cewar ta hanyar tattaunawa ce kadai za a kai ga warware dambaruwar siyasar kasar Venezuala lamarin da zai kai ga wanzar da zaman lafiya da sulhu a tsakanin al'ummar kasar.

A yau Laraba ne za a fara gudanar da zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin Venezuala da 'yan adawar kasar da suke neman kawo karshen mulkin shugaban kasar Nicolas Maduro a karkashin bakoncin gwamnatin kasar Dominica.  

Sep 13, 2017 12:20 UTC
Ra'ayi