• A Cikin Shirin Korar Baki: Amurka Zata Dakatar Da Bada Wasu Nau'in Visa A Wasu Kasashe

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta dakatar da bada wasu nau'in Visa ga wasu kasashe daga jiya Laraba a cikin shirin gwamnatin Donal Trump na korar baki daga kasar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto labarin daga bayanan da ma'aikatar ta fitar a ranar Talata da ta gabata, Labarin ya kara da cewa kasashen da abin ya shafa sun hada Cambodia, Eritaria, Guinea da kuma Salio.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka  Heather Nauert ta ce wadannan kasashen sun ki karbar yan kasashensu wadanda suka zo kasar ba tare da niyyar zama ba amma suka mike kafa suka ki fita daga kasar.

Nauert ta ce sakataren harkokin waye na kasar tuni ya aike da sakonni ga ofisoshin jakadancin Amurka a kasashen da abin ya shafa don fara aiki da umurnin . Sannan ta kara da cewa hana Visar sun bambanta a tsakanin kasashen, misali a kasar Eriteria, inda aka fi tsananta hanin,  za'a dakatar da bada Visar ga wadanda suke bukatar zuwa kasuwanci da yawon shakatawa. A kasar Guinea kuma Amurka ba zata dakatar da bada Visa ga ma'aikatan gwamnati da kuma iyalansu don harkokin kasuwa  yawon shakatawa da kuma karatu. A kasar Saliyo kuma za'a hana visa shiga Amurka ga jami'an ma'aikatar harkokin waje da kuma shige da fice.

 

Sep 14, 2017 05:29 UTC
Ra'ayi