Sep 19, 2017 05:43 UTC

A shekaran jiya ne shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bar nan Tehran zuwa birnin New York na Amurka don halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 inda ake sa ran a gobe Laraba zai gabatar da jawabinsa a gaban shugabannin kasashen duniya.

Taron na bana dai ya zo ne a daidai lokacin da duniya take fuskantar matsaloli da kalubale masu yawa wanda magance kowane guda daga cikinsu na bukatar aiki tare tsakanin kasashe. A halin yanzu dai ana iya cewa yankin Gabas ta tsakiya shi ne yankin da ke kan gaba wajen fuskantar matsaloli da kalubale masu yawan gaske da suke da alaka da irin tsoma bakin da manyan kasashen duniya suke yi a yankin wanda ko shakka babu shi ne ummul aba'isin din wadannan matsalolin, da suka hada da tsaurin ra'ayin addini, ta'addanci da kuma mamaya. A halin yanzu dai al'ummomin wasu daga cikin  kasashen yankin nan irin su Afghanistan, Iraki, Siriya, Yemen da Palastinu su ne kan gaba wajen cutuwa daga wannan bakar siyasa da manyan kasashen duniya da ta sanya su zama 'yan gudun hijira baya ga jinin da ake ci gaba da zubarwa.

Shugaban kasar ta Iran dai, a zaman babban zauren MDD da suka gabata ya gabatar da shawarar yadda za a kawo karshen rikice-rikice da yake-yake da ke gudana a duniya, wanda kuma aka amince da ita. To sai dai kuma ba a yi wani abin a zo a gani wajen cimma wannan manufar ba. Ta yadda har ya zuwa yanzu yankin nan na fuskantar barazana da tsoma bakin irin wadannan kasashe masu tinkaho da karfi musamman Amurka. Tsoma bakin da ke ci gaba da haifar da yakukuwa a yankin. Abin bakin cikin shi ne yadda wadannan kasashen ta hanyar fakewa da batun tabbatar da tsaron duniya suke ci gaba da sanya duniyar cikin mawuyacin hali na rashin tsaro.

Da dama dai suna ganin cewa matukar dai manyan kasashen duniya masu tinkaho da karfin suna son tabbatar da tsaron yankin nan, to wajibi ne su gudanar da siyasar su bisa tushe na girmama juna.

Ko shakka babu ci gaba da irin wannan bakar siyasa ta manyan kasashen duniya musamman siyasar mulkin mallakan Amurka na ci gaba da sanya duniya cikin hatsarin yaki. Daya daga cikin misalan hakan shi ne ci gaba da kada kugen yakin da Amurka take yi kan gwamnatin Koriya ta Arewa da kuma ci gaba da kafar ungulun da Amurkan take yi kan yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran da ci gaba da kakabawa kasar takunkumi. A daidai lokacin da duniya ta yi maraba da yanayin da aka samar bayan cimma yarjejeniyar nukiliya da ake ga zai share fagen aiki tare tsakanin Iran da sauran kasashen duniya wajen cimma manufofi da tsaron duniya musamman a fagen fada da ta'addanci wanda hakan lamari ne da zai amfani kowa, sai ga shi gwamnatin Amurkan ta yanzu tana kokarin sanya kafa ta shure dukkanin wannan kokari da aka yi.

A saboda haka ne fatan da ake da shi, shi ne cewa shugabannin duniyan da za su taro a wajen taron babban zauren MDD za su yi amfani da wannan dama wajen ganin an samar da hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyan duniya, wanda hakan na daga cikin abubuwan da shugaban na Iran zai fi ba su muhimmanci tsawon lokacin zamansa a birnin na New York.

Ra'ayi