Sep 30, 2017 11:17 UTC
  • 'Yan Shi'a Na Gudanar Da Juyayin Ranar Tasu'a A Kasashe Daban-Daban Na Duniya

Musulmi 'yan Shi'a a duk fadin duniya sun fara gudanar da ranar Tasu'a don tunawa da rana ta tara na watan Muharram rana guda kafin faruwar Waki'ar Karbala inda Imam Husain (a.s) da iyalai da sahabbansa suka yi shahada a Karbala.

A kowace shekara dai 'yan Shi'a suna gudanar da bukukuwan juyayin Tasu'a din da ta fado a ranar 9 ga watan Muharram, don tunawa da irin zaluncin da Banu Umayya suka yi wa Imam Husain (a.s) jikan Annabi kuma Imamin Shi'a na uku'yan Shi'a, da mabiyansa a Karbala a shekara ta 680 miladiyya.

Miliyoyin 'yan Shi'a din ne dai cikin bakaken kaya da sauran nau'oi na nuna bakin ciki da juyayi suke fitowa kan tituna da kuma taruwa a wajajen ibada don nuna juyayinsu inda kuma malamai da mawaka suke bayanin abubuwan da suka taru ga Imam Husain (a.s) da sauran zuriyar Annabi din.

A gobe Lahadi ne dai ake sa ran za a gudanar da bukukuwan juyayin Ashura, wato ranar da Imam Husaini (a.s) da mabiyansa su 72 suka yi shahada cikin mafi munin yanayi a Karbala a shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki (a.s).

 

Tags

Ra'ayi