Oct 02, 2017 11:23 UTC
  • Akalla Mutane 50 Sun Mutu Sakamakon Musayen Wuta A Las Vegas Na Amurka

Jami'an 'yan sandan kasar Amurka sun bayyana cewar alal akalla mutane 50 sun mutu kana wasu sama da 100 kuma sun sami raunuka sakamakon musayen wuta da ya faru a birnin Las Vegas na jihar Nevada na Amurka.

Kwamishinan 'yan sandan Las Vegas din Joseph Lombardo ya shaida wa manema labarai cewa ya zuwa yanzu dai sun tabbatar da mutuwar alal akalla mutane 50 da kuma wasu sama da 100 da suka sami raunuka a yayin hargitsin da ya faru a wani wajen rawa na birnin na suna Mandalay Bay Resort and Casino, inda ya ce ya zuwa yanzu dai an yi maganin lamarin.

Lamarin dai ya faru ne bayan da wani dan bindiga dadi ya bude wuta kan mai uwa da wabi inda bayan musayen wuta da suka yi da 'yan sanda, wasu majiyoyin 'yan sandan suka ce tuni sun sami nasarar hallaka shi.

Shugaban 'yan sandan dai ya bayyana cewa dan bindiga dadin shi ne Geary Danley wanda tuni suka hallaka shi, sai dai ya ce akwai wata mace da ake zaton suna tare da ita mai suna Mari Lou Danley 'yar shekaru 62 a duniya wacce kuma suna nemanta don tattaunawa da ita.

 

Tags

Ra'ayi