• MDD Ta Sanya Saudiyya Da Kawayenta Cikin Masu Take Hakkokin Bil'adama Saboda Yakin Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta sanya hadin gwiwan kasashen da suka kaddamar da yaki a kasar Yemen karkashin jagorancin Saudiyya cikin jerin sunayen kasashe masu take hakkokin bil'adama.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a jiya Alhamis ne Majalisar Dinkin Duniya ta sanya hadin gwiwan kasashen da suke yaki a kasar Yemen karkashin jagorancin kasar Saudiyyan cikin jerin sunayen kasashen da suke take hakkokin bil'adama saboda kashewa da kuma raunana alal akalla kananan yara 683 a Yemen da kuma hare-haren da suke kai wa makarantu da asibitoci a kasar Yemen din a shekarar bara ta 2016.

Kafin hakan dai kakakin MDDn ya bayyana cewar Majalisar Dinkin Duniya ba za ta ci gaba da yin shiru dangane da irin wannan aika-aika na Saudiyyan a Yemen ba.

Tun a shekara ta 2015 ne dai Saudiyyan da kawayenta suka kaddamar da yakin wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen din lamarin da yayi sanadiyyar mutuwa da raunana dubban al'ummar kasar ciki kuwa har da kananan yara da mata da tsoffi.

Tags

Oct 06, 2017 05:24 UTC
Ra'ayi