• Amurka Da Turkiyya Sun Tattauna Kan Takaddamar Bisa (Visa)

Sakatarorin harkokin wajen kasashen Amurka da Rasha sun tattauna ta wayar tarho kan takaddamar data kunno bayan soke bada bisa tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dilancin labaren Anadolu wanda ya rawaito labarin ya ce sakataran harkokin wajen kasar Mevlüt Cavusoglu ya tattauna da takwaransa na Amurkar Rex Tillerson kan takkadamar saidai ba tare da yin karin haske ba.

A ranar Lahadi data gabata ne ofishin jakadancin Amurka a Turkiyya ya sanar da dakatar da bada Bisa (visa) ga masu zuwa yawon bude ido da marasa lafiya da ‘yan kasuwa da kuma ma’aikata da dalibai.

Amurka ta ce ta yi hakan ne bayan Turkiyya ta daure wani ma’aikacin kasar da ke aiki da ofishin jakadancin Amurka a birnin Santanbul bisa zargin leken asiri.

Saidai bayan Turkiyya ta dauki mataki makamancin wannan na hana bada takardar bisa ga 'yan Amurka tare da kiran jakadanta da ke Amurka gida tare da bukatar Washington ta sauya matsayinta.

 

Oct 11, 2017 17:20 UTC
Ra'ayi