• Spaniya : Madrid Ta Ba Yankin Kataloniya Wa'adin Kwana 5

Gwamnatin Madrid ta baiwa shugaban 'yan a ware na Kataloniya, Carles Puigdemont, wa'adin kwanaki biyar don ya bayyana matsayinsa akan shelanta samun yancin kan yankin.

Majiyoyin daga gwamnatin sun ce Firayi ministan kasar ta Spaniya Mariano Rajoy ya baiwa Mista Puigdemont wa'adin har zuwa Litini don ya bayyana matsayinsa, idan kuma ya bayyana samun yancin yankin, gwamnatin Madrid za ta kara masa wani wa'addi na har zuwa ranar Alhamis 19 ko zai sake shawara.

Idan kuwa har zuwa wannan lokacin bai canza shawara ba to Madrid za ta yi aiki da doka mai 155 data ba gwamnatin Spaniya kwace yancin gashin kan yankin na Kataloniya.

Wannan dai shi ne rikicin siyasa mafi girma da kasar Spaniya ta taba fuskanta a shekaru masu yawa.

Tun da farko dai Firayi ministan Spaniya din Mariano Rajoy ya bukaci shugabannin yankin na Kataloniya dasu bi tsarin doka, a yayin da suke shirin sanar da samun ‘yancin kai.

 

Oct 11, 2017 18:04 UTC
Ra'ayi