• Shugaban Hukumar Palasdinawa Zai Kai Ziyara Zuwa Yankin Zirin Gaza Na Palasdinu

Shugaban Hukumar Cin Kwarya-kwaryar Gashin Kan Palasdinawa zai kai ziyarar aiki zuwa yankin Zirin Gaza domin zantawa da kungiyar Hamas da nufin warware sabanin da ke tsakaninsu.

Zakariyya Al-Lagha jami'in a kungiyar Fatah a yau Alhamis ya bada labarin cewa: Shugaban hukumar Palasdinawa Mahmud Abbas zai kai ziyarar aiki zuwa yankin Zirin Gaza da nufin tattauna batun sabanin  da ke tsakanin kungiyar Hamas da hukumar cin gashin Palasdinawa domin kawo karshen dambaruwar siyasar da ke tsakanin al'ummar Palasdinu.

Hukumar Cin Gashin Kan Palasdinawa karkashin fira ministan hukumar Rami Hamdullahi a makon da ya gabata ya ziyarci yankin Zirin Gaza tare da gudanar da zaman tattaunawa da kungiyar Hamas da nufin neman hanyar warware sabanin da ke tsakanin bangarorin biyu.  

Tags

Oct 12, 2017 11:51 UTC
Ra'ayi