• Amurka Ta Sanar Da Janyewarta Daga Hukumar UNESCO

Amurka ta sanar da janyewarta daga hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kimiya da al’adu (UNESCO) saboda zargin da take yi wa hukumar na rashin goyon baya da kuma nuna kyama ga haramtacciyar kasar Isra’ila.

Amurkan cikin wata sanarwa da Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a yau din nan Alhamis, ta ce ta sanar da Majalisar Dinkin Duniyar ficewarta daga wannan hukuma.

Kafin hakan dai Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Amurka Heather Nauert ta sanar cewa Washington za ta janye jakadarta daga hukumar ta UNESCO da take da helkwata a birnin Paris na kasar Faransa saboda irin kyamar "Isra'ila" da ake yi a hukumar. Sanarwar ta kara da cewa Amurka za ta kafa wata tawaga da sanya ido da za ta ci gaba da wakiltanta a hukumar.

Kafin haka ma dai a shekarar 1984 lokacin mulkin Ronald Reagan saboda abin da ta kira nuna goyon baya ga hukumar take yi ga tsohuwar tarayyar Sobiyeti.

Gwamnatin Amurkan ma dai ta sanar da cewa akwai yiyuwar za ta fice daga hukumar kare hakkokin bil'adama ta MDD (UNHRC) saboda zargin da suke wa hukumar cewa tana nuna kyama ga Isra'ilan.

Tags

Oct 12, 2017 17:22 UTC
Ra'ayi