• Siyasar Trump Kan Iran Na Kara Tabbatar Da Cewa Amurka Ba Abar Yarda Ba Ce

A ranar 14 ga watan Yulin 2015 ne, bayan kokari da tattaunawa na tsawon shekaru da nufin cimma matsaya kan shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran, aka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya (wato kasashen Amurka, Rasha, China, Birtaniyya, Faransa bugu da kari kan kasar Jamus).

Kasashen duniya da daman gaske sun yi maraba da sanya hannu kan wannan yarjejeniya wacce ake kira da JCPOA ko kuma Barjam (a farisance) in ban da wasu 'yan tsiraru irin su Saudiyya da HKI, to sai dai a halin yanzu sakamakon ci gaba da kasar ungulu da rashin cika alkawarin Amurka, yarjejeniyar tana fuskantar matsala watakila da ma kawo karshenta wanda da dama sun yi amanna da cewa babu wani da zai amfana daga hakan.

Bayan makonni na bakar farfaganda, a ranar Juma'ar da ta gabata ce fadar White House ta Amurka ta fitar da wata sanarwa da ta kira Sabuwar Siyasar Shugaban Amurka Kan Iran Da Yarjejeniyar Nukiliya. Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Amurkan, cikin wani jawabi da yayi a daren Juma'ar, ya gabatar da wasu tuhumce-tuhumce marasa tushe a kan Iran da kuma zargin Iran da karya yarjejeniyar nukiliyan yana mai bayyana yarjejeniyar a matsayin daya daga cikin yarjejeniyoyi mafiya muni da Amurka ta taba sanya wa hannu tsawon tarihinta, yana mai barazanar kawo karshen yarjejeniyar a duk lokacin da ya ga ya dace, kamar yadda kuma ya sanar da wasu sabbin  takunkumi kan Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar.

Jim kadan bayan gama wannan jawabin dai, shugaban kasar Iran, Dakta Hasan Ruhani, cikin wani jawabi da yayi kai tsaye ta gidan talabijin din kasar Iran yayi watsi da wadannan kalamai na shugaban Amurkan, sannan kuma yayi karin bayani dangane da irin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Iran da Amurka ta yi bugu da kari kan irin ayyukan t a'addanci da cutarwar da Amurka ta yi wa al'ummar Iran tsawon tarihi, daga nan sai ya ce: Al'ummar Iran dai ba wata al'umma ce wacce saboda wasu kalamai na rashin mafadi za ta mika kai ga wasu masu tinkaho da karfi da girman kai ba. Ya zuwa yanzu al'ummar Iran ba ta taba mika kai sannan kuma a nan gaba ma ba za ta taba mika kai ga masu tinkaho da karfi ba.

To masana dai suna ganin a halin yanzu da lamarin ya kai ga haka, hanyoyi dai guda biyu ne suka saura: Ko dai kasashen duniya musamman wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar su tsaya kyam wajen kare ta, don kuwa ita wannan yarjejeniyar wani bangare ne na kudurin Kwamitin Tsaron MDD mai lamba 2231 da duniya ta yarda da ita ko kuma su mika wuya ga siyasar rashin hankali na shugaban Amurka.

Tun kafin wannan lokacin da ma bayan hakan, Jamhuriyar Musulunci ta Iran  ta sanar da cewa ba za ta zamanto mafarin yin watsi da yarjejeniyar nukiliyan ba, don kuwa bisa koyarwar Musulunci cika alkawari da yarjejeniyar da aka cimma wajibi ne, to amma fa matukar ba a kiyaye hakkokinta ba, kamar yadda ya zo cikin yarjejeniyar, to kuwa za ta yi watsi da ita sannan kuma za ta dawo ta ci gaba da dukkanin ayyukanta na nukiliya daga inda ta tsaya.

A mahangar al'ummar Iran dai gaba da adawar Amurka a gare su ba wani sabon abu ba ne. A hakikanin gaskiya Amurka dai tana adawa ne da tsarin Musulunci da ke mulki a Iran don kuwa ya kawo karshen bakar mulkin mallakar da take yi wa al'ummar Iran da tsoma baki cikin harkokinsu. Don haka ne ma da dama daga cikin al'ummar Iran din ba su yi mamakin abin da shugaban Amurkan ya fadi ko kuma matakin da ya sanar zai dauka ba, wanda hakan ma ya kara musu hadin gwiwa da kuma karfi ne wajen ci gaba da riko da tafarkin da suke kai.

Ko shakka babu matakan da Trump yake dauka kan Iran da ma sauran batutuwa na dama wani lamari ne da ke kara sanya Amurkan zama saniyar ware a idon duniya da kuma tabbatar da cewa lalle ita ba abar yarda ba ce.

Oct 16, 2017 04:37 UTC
Ra'ayi