• WFP: Babu Adalci Wajen Raba Abinci A Duniya

Hukumar abinci ta duniya ( WFP) ta fitar da wani rahoto a jiya talata da a ciki ta bayyana rashin daidaito akan farashin abinci a duniya.

Wani sashe na rahoton ya ce; A birnin Newyork na Amukra farashin kwanon abinci daya yana kamawa akan dala 1.2, yayin da a Sudan farashin ya ke kai wa dala 321.

Rahoton ya kuma yi ishara da karfin saye na kudaden a cikin kasashe daban-daban na duniya, wanda yake da tazara daga wata kasa zuwa wata.

Manajan zartarwa na hukumar abinci ta duniya David Bessley ya ce; kwararrun kungiyar ne suka gudanar da bincike a cikin kasashe daban-daban na duniya dangane da karfin sayen kwano daya na abinci.

Har ila yau hukumar ta yi ishara da yadda talauci yake karuwa a duniya saboda yake-yake da rashin tabbaci na siyasa dakuma sauyin yanayi.

Tags

Oct 17, 2017 12:30 UTC
Ra'ayi