Oct 28, 2017 06:29 UTC
  • Amurka Ta Kakabawa Wasu Kamfanonin Kera Makaman Rasha Takunkumi

Amurka ta fitar da jerin sunayen wasu kamfanonin kera makaman Rasha su 39, wanda ta haramta yin ciniki da su.

Daga cikin kamfanonin da akwai na sayar da makamai da motocin soji irinsu Rosoboronexport da kuma shahararen kamfanin kera makamai na Kalachnikov. 

Wata sanarwa da gwamnatin Amurkar ta fitar ta ce duk wani kamfani da ya yi mu'amula da wadandan kamfanonin zai fuskanci takunkumi daga Amurka.

A watan Yuli da ya gabata ne majalisar dokokin Amurka ta amunce da wannan dokar, duk da adawa da shugaban kasar Donald Trump ke yi da ita.

Wani jami'in gwamnatin Amurkar ya ce wannan kudirin na majalisar dokoki da gwamnati na da manufar yin aiki da kudiri mai lamba 231 na dokar domin daukar mataki kan Rasha akan rikicin Ukreine, da kutse ta hanyar internet da kuma take hakkin bil adama.

A watan Janairu na shekara mai zuwa ne takunkumin zai fara aiki.

Tags

Ra'ayi