• Paparoma Francis Ya Bayyana Damuwarsa Kan Shirin Amurka Na Mayar Da Ofishin Jakadancinta Zuwa Qudus

Shugaban darikar Katolika ta mabiya addinin kirista ta duniya Paparoma Francis ya bayyana tsananin damuwarsa kan shirin gwamnatin Amurka na mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin Qudus domin birnin ya kasance fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

A jawabin da ya gabatar a yau Laraba: Shugaban darikar Katolika ta mabiya addinin Kirista ta duniya Paparoma Frnacis ya bukaci girmama birnin Qudus kamar yadda take a halin yanzu tare da mutunta kudurorin Majalisar Dinkin Duniya kan birnin na Qudus.

Paparoma Francis ya kara da cewa: Birnin Qudus mallakin dukkanin addinai guda uku ne wato Musulunci, Kiristanci da Yahudanci, don haka Paparoma Francis ya bayyana cewar yana gudanar da addu'a birnin na Qudus ya ci gaba da zama birni mai daraja kamar yadda take a idon al'ummar yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.

Duniya tana ci gaba da yin gargadi kan matsayin gwamnatin Amurka na kokarin maida ofishin jakadancinta zuwa birnin Qudus domin birnin ya zame fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila maimaikon Tel-Aviv, kuma a yau Laraba ne shugaban Amurka Donald Trump zai fayyace matsayin gwamnatinsa na maida ofishin jakadancin kasar zuwa birnin Qudus a jawabin da zai gabatar.

Tags

Dec 06, 2017 18:57 UTC
Ra'ayi