• Shugaban Kasar Amurka Ya Sanar Da Qudus A Matsayin Fadar Mulkin Gwamnatin H.K.Isra'ila

Shugaban kasar Amurka ya yi furuci da kasancewar birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

A jawabin da ya gabatar dazu-dazun nan a yau Laraba: Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi furuci da Qudus a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila duk da kiraye-kirayen da duniya ta masa kan ya nisanci wannan furuci saboda ya yi hannun riga da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.

Har ila yau shugaban na Amurka ya kuma bada umurni ga ma'aikatar harkokin wajen kasar kan ta fara gudanar da shirye-shiryen mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Qudus daga Tel-Aviv.

A cikin jawabinsa Donald Trump ya bayyana cewa: Dukkanin siyasar shugabannin Amurka da suka gabata na kin yin furuci da Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, siyasa ce da bata yi nasara ba, don haka wannan mataki da ya dauki shi ne siyasar da ta dace kuma wadda zata haifar da zaman lafiya a cewarsa.

 

Tags

Dec 06, 2017 19:06 UTC
Ra'ayi