• An Fara Taron Hukumar Tsaron Da Hadin Kai Na Kasashen Turai

Hukumar tsaron da hadin kan kasashen turai sun fara gudanar da taro da nufin bincike kan tabbatar da dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar Ukrene.

Ministocin harakokin wajen kasashe 57 manbobi na wannan hukuma da suka hada da Rex W. Tillerson saktaren harakokin wajen Amurka, da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov sun hadu kan tebiri guda yau alkhamis a birnin Vienna da nufin tattauna maudu'in aikin dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar Ukrene.

Zaman da aka saba gudanarwa ko wata shekara, wanda kuma a bana kasar Australiya ne ke karbar bakuncinsa, ya zo ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin kasashen Rasha da Amurka tayi rauni.

Hukumomin birnin Masco ne dai suka bada shawarar tura dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar ta Ukrene domin kare masu sanya ido a yarjejjeniyar sulhun da aka cimma,kimanin mutane 600 ne na hukumar tsaro da hadin kai kasashen turai aka dorawa yaunin sanya ido kan yarjejjeniyar sulhu tsakanin gwamnati da 'yan tawayen gabashin Ukrene.

Bisa alkaluman da MDD ta fitar, daga shekarar 2014 zuwa yanzu rikicin gabashin kasar Ukrene din ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 10.

Dec 07, 2017 19:00 UTC
Ra'ayi