• An Kai Hari Kan Taron Yahudawa A Birnin Amsterdam

Wani mutum dauke da tutar Palastinu sun kai hari kan wurin taruwar sahayuna a birnin Amsterdam na kasar Holland.

Tashar telbijin din IT5 ta kasar Holland ta habarta cewa wani mutum da ya rufe fuskarsa dauke da tutar Palastinu cikin kabbara ya kai hari kan wani gidan cin abinci na yahudawa a tsakiyar garin Amsterdam tare da farfasa gilasan hotel din a wannan alkhamis, saidai rahoton ya ce babu wani mutum guda da ya jikkata sanadiyar harin.

Rahoton ya ce maharin ya shiga hanun 'yan sanda a yayin da yake kokarin fidda tutar haramcecciyar kasar Isra'ila daga saman gidan Hotel din.

Wannan hari dai na zuwa ne kwana guda kacal, bayan da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ayyana birnin Qudus a matsayin babbar birnin HKI, kudirin da duniya ta yi alawadai da shi.

Dec 07, 2017 19:00 UTC
Ra'ayi