Dec 10, 2017 07:39 UTC
  • MDD: A Kaucewa Kuskuren Lissafi Akan Korea Ta Arewa

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da bayani da a ciki ya bayyana wajabcin bude kafar tataunawa da Korea ta Arewa domin rage zaman dar-dar a yankin.

Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Jefferey Feltman ya ziyarci Korea ta Arewa inda ya gana da ministan harkokin wajenta Ri Yong-ho. A yayin tattaunawar Feltman ya yi kira da aiki da kudurorin Majalsiar Dinkin Duniya, sannan ya kara da cewa kungiyoyin kasa da kasa a shirye suke su samo hanyoyin ruwan sanyi domin warware matsalar yankin.

 A nata gefen, gwamnatin Korea Ta Arewa ta bayyana ziyarar ta Feltman da cewa ta yi amfani.

Jawaban da shugaban kasar Amurka Donald Trump yake yi akan Korea Ta Arewa suna taimakawa wajen haddasa zaman dar-dar a yankin.

Tags

Ra'ayi