Dec 10, 2017 19:07 UTC
  • Amurka Ta Ce: Shugaba Trump Ya Shawarci Kawayen Amurka Kafin Daukan Mataki Kan Qudus

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta bayyana cewa: Shugaban Amurka Donald Trump ya shawarci kawayen kasarsa a yankin gabas ta tsakiya kafin daukan matakin shelanta Qudus a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Tashar talabijin ta Al-Hadath ta bayyana cewa: Jami'a a ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Erica Chiusano ta bayyana cewa kafin shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauki matakin shelanta Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sai da ya tattauna da kasashen da suke kawance da Amurka a yankin gabas ta tsakiya musamman kasar Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra'ila.

Erica Chiusano ta kara da cewa: Trump ya kuma buga wayar tarho wa dukkanin shugabannin kasashen da suke kawance da Amurka a yankin ta gabas ta tsakiya tare da jaddada bukatar samun goyon bayansu kan shirin da ya sanya a gaba na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila gami da maida ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin na Qudus daga Tel-Aviv, inda wasu suka dan yi tsokaci kan bukatar.

Erica Chiusano ta kuma bada labarin cewa: A halin yanzu haka shugaba Trump ya kafa wata tawagar mutane domin gudanar da ziyarar aiki zuwa yankin gabas ta tsakiya da nufin tattaunawa da shugabannin kasashen Larabawa kan batun na Qudus.

Tags

Ra'ayi