Dec 13, 2017 06:01 UTC
  • Rahoton Amnesty Kan Zargin Turai Da Taimakawa Cin Zarafin Bakin Haure A Libya

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty International, ta zargi gwamnatocin kasashen turai da hannu a cin zarafin da ake yi wa bakin haure da 'yan gudun hijira a Libiya.

Rahoton da Amnesty ta fitar ya ce a kokarin ta na dakile kwararar bakin haure, kungiyar tarayyar Turai tana taimaka wa wajen azabtarwa da zaluncin da ake wa dubun dubatar bakin hauren da 'yan gudun hijira a gabar tekun Libiya.

Amnesty ta ce kudaden kungiyar tarayyar Turai suna zuwa ga hukumomin da ke aiki da mayaka da kuma masu safarar mutane, a yunkurin da take na dakile kwararar bakin hauren zuwa turai ta hanyar tekun  Bahar Rum.

Rahoton ya ce tun daga karshen shekara 2016 data gabata, kasashe mambobin kungiyar ta EU, sun dauki matakai iri daban-daban na rufe hanyoyin kwararar bakin haure tun daga Libya zuwa tsakiyar tekun Bahar Run ba tare da yin la'akari ba da abunda hakan zai iya haifar.

Darektan kungiyar ta Amnesty kan kasashen Turai, John Dalhuisen, ya ce sakamakon wadanan matakai na kasashen turai, dubun dubatar mutane ne ake tsare da su a cikin mayuyacin hali.

Kungiyar tarayyar Turai dai ta bayar da jiragen ruwa da horaswa da kuma kudi ga jami'an tsaron gabar tekun Libiya, saidai a cewar Amnesty  jam'ian tsaron suna aiki da 'yan daba masu laifi da kuma masu safarar mutane, wannan kuma da sanin jami'an kungiyar tarayyar Turai.

A hirarsa da kamfanin dilancin labaren AFP, Mista Dalhuisen, ya fi zargin hukumomin birnin Roma, wadanda a cewarsa suke hadin gwiwa da daukan tsauraren matakai da gwamnatin hadaka ta Libya.

Wannan kuma a cewarsa ya sanya Italiya a cikin wani yanayi na kin sauke yaunin kasa da kasa da ya rataya akanta musamen wanda ya shafi haramta azabtarwa.

Jami'in ya kara da cewa karfafa matakan na gwamnatin Roma da kuma yarjeniyoyin da take da Tripoli ya taimaka wajen rage kwararar bakin hauren : tsakanin watan Yuli zuwa Disamba yawan bakin hauren da suka sauka a Italiya ya rage da sama da kashi 65% idan aka kwatanta a daidai irin lokacin a tsakanin shekarun 2014 - 2016.

Amma duk da haka AMnesty ta ce a hirar data yi da wasu bakin hauren da 'yan gudun hijira, kan zargin cin zarafin, dayewa daga cikinsu sun ce tabas ana azabtar dasu tare da tsarewa ba bisa ka'ida ba da kuma sanyasu aikin karfi.

Amnesty ta kuma zargi jami'an gabar ruwa Libya da hannu a safara bil adama, suna kuma karbar kudi a hannun balin hauren dan fitar dasu daga kasar ta Libya.

Kungiyar kuma ta zargi jami'an gabar ruwa da kawo cikaswa aikin ceton bakin haure da kungiyoyin agaji ke yi a tekun na Bahar Rum.

Alkamuman da hukumar kula da bakin haure ta MDD wato HCR, ta fitar sun ce bakin haure kimanin 3,000 ne suka gamu da ajalinsu a cikin watannin 11 na wannan shekara a kokarinsu na shiga Turai.

Babban batun da kuma ya kunno kai a baya bayan nan wanda kuma ya tayar da hankalin duniya matuka shi ne na cinikin bakin haure tamakar bayi a kasar ta Libya, lamarin da ya tilasta wa kasashen Afrika da dama kwashe mutanensu daga kasar.

Kungiyar tarayya Afrika ta sanar da wani shirinta na hadin gwiwa da hukumar kula da bakin haure ta MDD na kwashe bakin hauren 20,000 daga kasar ta Libya a cikin makwanni shida.

Tuni dai aka fara aiwatar da shirin, inda daruruwa bakin hauren 'yan Afrika suka koma kasashensu na asali, kuma dayewa daga cikinsu sun tabatar da batun da ake na cin zarafi da azabtarwa da kuma cinikin bakn hauren a kasar ta Libya.

Tags

Ra'ayi