Dec 24, 2017 06:25 UTC
  • Yan Majalisar Dokoki Amurka 24 Sun Bukaci Gwamnatin Trump Ta Dauki Matsayi Kan Iran

Wakilan majalisar dokokin kasar Amurka 24 yan jam'iyyar Republican sun rubuta wasika zuwa gwamnatin shugaba Donald Trump kan abin da suka kira sabuwar yarjejeniyar Nukliyan da kasar Iran ta yi.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya bayyana cewa, a jiya Asabar ne wakilan jam'iyyar Republican 24 karkashin jagorancin Lee Zeldin sun rubutawa ministan harkokin wajen Amurka Rex W. Tillerson, da ministan tsaron kasar James Matthews da kuma Mike Pompeo shugaban hukumar CIA suna neman su bayyana matsayinsu kan sabawa kudurin MDD kan shirin makamashin nukliyan kasar Iran wanda kasar Iran din ta yi har sau 8 a fadinsu.

Wadannan yan majalisar jam'iyyar republican sun gabatar da wannan zargin ne ga gwamnatin Amurka a dai-dai lokacin da hukumar IAEA wacce aka dorawa nauyin kula da wannan bangaren na kudurin, ta bada rahoto har sau 9 kan cewa Iran bata sabawa wannan kudurin ba. 

Banda haka a ranar Talatan da ta gabata ce kwamitin tsaro na MDD ta gudanar da zama, ba tare da hallatar jakadiyar Amurka a zaman kwamitin ba, gaba dayan mambobin kwamitan sun tabbatar da cewa babu wani wurin da Iran ta sabawa wannan kudurin.

Tags

Ra'ayi